duhu da haske
Abin da kake kira da "Haske" da abin da kake kallo a matsayin "Duhu", duka sassa ne guda biyu na makamashi guda daya (Universal Energy).
Kafin ka yi saurin yanke hukunci, tsaya ka saurare ni da kyau domin zan baka abinda baka taba ji ko sanin haka yake ba.
Abun nufi kenan akwai wani makamashin a tsakaninsu, wanda wannan makamashin tsaka-tsaki ne, amma yana rarrabuwa gida biyu ne kawai domin halitta ta fuskanci kanta.
Dole ne ka fahimci cewa, shi "Haske" (Light) shine asalin sani wanda yake me tsarki, kamar dai bin hanyar dai dai.
Shi kuma abin da kake gani a matsayin kishiyarsa, asalin wannan sani ne amma wanda ya yi nauyi ya koma cikin duhu, zamu iya Kiran wannan da kaucewa hanyar dai dai kenan?
Wannan ba yaki ba ne tsakanin wasu abubuwa biyu mabanbanta, a’a, yanayi ne na mizanin sanyi da zafi (Polarity). Kamar yadda sanyi ba makiyin zafi ba ne, illa dai kawai duka maki ne a jikin ma’aunin zafi guda daya. Haka abin yake a duniyar makamashi; wannan matsayi ne na daban, wancan ma matsayi ne na daban a mizanin girgizar sauti.
Duhu ba ya adawa da haske; a maimakon haka, shi ne ma yake tallafa masa.
Duhu ne yake ba ka damar ganin haske, kuma haske ne yake ba duhu ma’ana. Wannan shi ne babban darasin da makarantun boyayyen ilimi suke koyarwa, wanda tsofaffin akidu ba za su iya bayyana maka ba.
Asalin "Duhu" ko abin da kake kallo a matsayin rauni, shi ne mantuwa, mantawar da mutum yake yi na asalin wanda shi kansa yake, ko kuma Ka manta ma da abinda donshi aka halicceka. Shi ne karkata zuwa ga son jiki, nauyin zuciya, da kuma jin cewa ka rabu da asalin Tushenka.
A cikin kowane mutum, akwai wadannan bangarori guda uku da suke gudanar da rayuwarsa. Akwai Zuciyar Sha’awa wadda take tura ka zuwa ga abubuwa ba tare da lura da sakamako ba, sannan akwai Hasken Sani wanda yake neman daidaito da haske a kowane lokaci. Daga karshe akwai Mizanin Shari’a, wanda shi ne ikon da yake kokarin daidaita wadannan bangarori biyu domin rayuwarka ta zauna daidai.
Dukkan wadannan bangarori suna da muhimmanci domin idan babu duhu (shadow), ba za ka taba samun bambanci ba.
Idan kuma babu bambanci, ba za a taba samun "Sani" (Consciousness) ba.
Ba a turo ka wannan duniya don ka yi fatali da duhunka ba, an tura ka ne domin ka tace shi, ka mayar da shi haske. Kai ne kadai makamashin da yake da ikon hada abin da aka raba.
Kai ne hasken, kuma kai ne ke da ikon sarrafa duhunka. Wannan gaskiya ce wacce mutane kalilan ne suke shirye don fahimtarta, kuma kana da dukkan madawwamin lokaci don ka gane hakan, domin ruhinka ba ya mutuwa.
A wannan shafi, burina shi ne na bude maka idonka basira ka daina kallon duniya a matsayin wajen yaki, sai dai a matsayin wajen neman daidaito da sanin kai.
Comments
Post a Comment