me yasa bazaka iya suffanta mutuwa ba bayan kamutu??
Me Yasa Ba Za Ka Taba Iya Siffanta "Mutuwa" A Cikin Tunaninka Ba?
Saurara da kyau zuwa ga wannan boyayyen ilimi na Metaphysics.
Ka taba tsayawa ka yi lura da wani babban al’ajabi da yake a boye?
Akwai wani abu mai ban mamaki game da yadda kwakwalwarka take aiki, za ka iya siffanta yadda ake "Mutuwa" (Dying), amma ba za ka taba iya siffanta yadda yake idan mutum "Ya Mutu" (Being Dead) ba.
Wannan ba wai tsoro ba ne da kake ji a zuciyarka; wannan wata iyaka ce ta Consciousness (Wayewar Kai) wacce aka halicce ka da ita.
Duk wani hoto da za ka halitta ko kayi tunaninsa a zuciyarka game da mutuwa, ko yadda kake tunani bayan ranka, har yanzu dai akwai Wayewar Kai (Awareness) a cikinsa.
Ma'ana, a cikin tunanin naka, kai ne kake kallon gawar taka, ko kake kallon mutane suna kuka. Muddin akwai "Mai Kallo" (The Observer) a cikin wannan tunanin, to ashe ba ka mutu ba ke nan. Wayewar kanka ba ta da ikon siffanta rashin kanta, domin duk siffar da za ta bayar, sai ta sanya kanta a ciki tana kallo.
Ilimin metaphysics ya nuna mana cewa hankalinka yana iya siffanta hakika (Reality) ne kawai a inda shi kansa yake wanzuwa. Wannan ba hatsari ba ne; tsari ne na halitta wanda yake tabbatar maka da cewa kai ba wannan gangar jikin ba ne, kai wani madauwamin haske ne na wayewa.
Talakawan mutane (Marasa sani) suna rayuwa cikin tsoron abin da ba su sani ba, amma kai ya kamata ka gane cewa rashin iya siffanta mutuwa shaida ce ta cewa Rayuwa ita ce gaskiyar da Kake ciki a yanzu.
Kar ka Taba Mantawa Ilimi Shi ne Arziki.
Makamashin da yake cikin zuciyarka ba a halicce shi don ya gushe ba, shi ya sa ma ba zai taba iya hango kansa a matsayin "babu" ba.
Duk abin da muke bukata don yin nasara da samun kwanciyar hankali yana kusa da mu; jahilcinmu ne kawai yake tsare da mu daga gane asalin wanene mu. Rike wannan ilimin, domin shi ne babban arzikin da za ka mallaka.
Comments
Post a Comment