crypto believe🙏
Idan ka ɗauki crypto a matsayin sana'a kuma kayi abubuwan ka da jajircewa, ko bakayi kuɗi ba, zaka samu rufin asiri. Sai dai in haƙurin ka ya gaza. Kayi duba a shekaru biyar zuwa shida da suka wuce, da yawan waɗanda suke cikin crypto a yanzu N3k sha'awa take basu. Amma saboda consistency zuwa yanzu duk wanda suka fara crypto 2020 zuwa yanzu zaiyi wahala kaga mutun in baiyi kuɗi ba ya samu rufin asiri dashi indai ya maida hankali kuma bai sare ba, yaci gaba da ƙara ilimi da experience. Masu bincike suka ce; idan ka ɗauki abinda kake so ka koya da mahimmanci, zaka ware masa awa 3 zuwa 5 a kowacce rana na tsawon wata 3 kullum kana karatu, da nazari akansa. Ba tare da kana saka wasa ba. Shiko Malcolm Gladwell cewa yayi acikin littafin sa na 'Outliers' zai ɗauke ka awa 10,000 kana jarraba abinda ka koya kafin ka ƙware akansa, misali kamar ka zama irin Bill Gates a fannin iya Programming. A zance na adalci, zai ɗauke ka wata uku kullum kana ware awa 2-5 kana karatu akan Cryp...