Kayi Al. heri cikin kulawa
Dalilin da ya sa kake shan wahala a rayuwa ba wai don ba ka da amfani ba ne, a'a, saboda ma ka cika amfanin ne da yawa.
A ilimin Metaphysics, duk lokacin da ka bayar da makamashinka (energy) ga wanda bai shirya karba ba, kana dasa wa kanka gaba ne. Wanda haka ke nufin cewa kai ne da kanka kake samar wa kanka makiyi ta hanyar abin da kake yi (ko da kuwa hakan alheri ne a zahiri).
Ilimin Dark Psychology ya tabbatar mana da cewa, mutane ba sa girmama wanda yake taimakonsu a kowane lokaci; maimakon haka, tsoronsa suke ji, kuma daga baya su dawo jin haushinsa, har su kai ga kulla masa makirci domin su kawar da shi.
To wannan shi ne sirrin da ya sa "Nice Guys" ko mutanen kirki suke zama na karshe wato mutanen da akafi yaudara da wayo, yayin da azzalumai masu amfani da dabarun Robert Greene suke cin nasara.
Wannan ba irin ko wacce magana ba ce; doka ce ta tarihi wadda ta shafi Sarakuna, Janar-janar na yaki, da manyan ’yan kasuwa.
A karkashin dokar kimiyyar tunani, duk lokacin da ka taimaki mutum, kana nuna masa rauninsa ne, kuma hakan yana taba girman kansa (ego). Maimakon ya gode maka, zuciyarsa sai ta fara neman hanyar da zai karkata wannan iko da kake da shi a kansa wato ya Fara tunanin mallarka komai naka.
Shi ya sa kake ganin dalibi yake kifar da teburin malamin da ya koya masa sana'a, ko wanda ka taimaka wa ya koma yana yaɗa jifanka da sharri. Kyauta ko taimako idan ba a yi ta da lissafin ilimi ba, takobi ce da kake mika wa makiyinka domin ya soke ka.
Abin da nake son ka gane shi ne, wannan duniyar ba a kan kyautatawa take tafiya ba, a kan ma'aunin iko take. Yayin da kake bata lokacinka wajen zama bango ga kowa, wasu suna amfani da rauninka wajen gina taswirar yadda za su tunkuye ka.
Da zarar ka fita daga layin zama mai taimako maras kan gado, za ka fara ganin canji a yadda mutane suke kallonka.
Ba wai ina ce maka ka daina alheri ba ne; ina ce maka ne kayi a hankali kada ka zama lamba ta biyu a rayuwar wadanda suke kallonka a matsayin tsani. Idan ka fahimci wannan sirrin na Dark Psychology, rayuwarka ba za ta taba komawa yadda take ba, domin za ka daina ba da makamashinka ga inda ba za a yi girbin girmamawa ba.
Comments
Post a Comment