Kin tace

Kylian Mbappé ya taba fada a wata hira yace "Sa’adda nake dan shekara takwas, tuni na fara koyon yadda ake bada hira (interview) da kafafen yada labarai, domin na san wata rana zan yi."

Wannan duniyar da kake rayuwa a cikinta gaskiya ce, amma ba ita ce gaskiyar karshe ba. 

Ajiye wannan rubutun a wayarka yanzu, domin darasi ne mai muhimmanci da zai taimake ka wajen bayyana abubuwan da kake bukata a rayuwa!

Ka gane wannan, Mun riga mun shiga wata na biyu na shekara. Haka ne, wannan duniya gaske ce. Kana iya taba ta, gani, da jin ta Babu karya akan haka. Jikinka yana nan; abubuwa, mutane, wurare, komai yana bayyana a matsayin abu mai karfi da za a iya taba wa.

Amma wannan duniyar gaskiya ce kawai a fakaice. Tana canzawa, tana tsufa, kuma tana mutuwa. Tana bin lokaci, sarari, da rabe-raben rayuwa. Amma ba ita ce gaskiyar karshe ba, domin ita gaskiya ba ta canzawa.

Gaskiya ba ta mutuwa, ba ta gushewa, kuma ba ta dogara ga komai ba. Gaskiya ita ce ruhi, tsantsar sani, abin da yake bayan jikinka da kuma azancinka na jiki.

Wannan duniya kamar hoton da aka haska ne (projection). Fim din nan "The Matrix" ya bayyana hakan dalla-dalla. Wannan duniya ba ta wanzu da kanta ba. Babu abin da yake nan wanda bai riga ya wanzu a duniyar ruhi ba (astral plane). 

Duniyar ruhinka ce ta halacci duniyarka ta zahiri, kamar yadda kai ma kake a siffar ruhin da ya mallaki gangar jiki.

Rayuwarka ta riga ta wanzu tun kafin a haifi jikinka. Ba za ka taba sa ran cimma manyan abubuwa ba tare da ka mayar da hankali ga fannin ruhinka ba, walau da saninka ko ba tare da saninka ba.

Lokacin da Kylian Mbappé ya fadi haka a hirarsa, babu wani abu da ya kai wannan zurfi, wato daidaita kanka da wani lokaci na daban inda nan gaba ta riga ta faru, domin wannan lokacin dakayi tunani ya zama gaskiya.

Tunani yana samar da halitta, ba ka da masaniya kan karfinsa. Ba maganar addu’a ko roko ba ne. Yin tunani da hango nasara (visualization) shi ne haduwa da waccan siffar taka da ke cikin filayen damarmaki marasa iyaka, wato siffar nan taka wadda ta riga ta cimma abin da kake bukata.

Kuma tunani ko hango nasara ba abin da kamus (dictionary) yake gaya maka ba ne.
 
Abin da kake gani gaske ne, amma ba shi ne gaskiyar karshe ba. Kuma idan ka gaya mini cewa takardun makaranta ko lissafin kudi kodai wani abu da kake iya gani da idonka sune gaskiya, to ba ka fahimci darasin nan ba.

Wannan sako an nufi wani sashe na daban ne na jikinka. Kada ka taba mantawa, duniyar ruhi ita ce asalin gaskiya. Ta fi karfin wannan duniyar nesa ba kusa ba. Kuma a X ma, ina so in fara wannan tafiya tare da kai. Kada ka manta ka bini ni a can ma.

Babu abin da zai iya bayyana a zahiri ba tare da tushe na ruhi ba. 

Peace and blessings

Comments

Popular posts from this blog

duhu da haske

me yasa bazaka iya suffanta mutuwa ba bayan kamutu??

Gaskiyar Magana Akan pi network Dual 2 value