me ye Amfanin Addua bayan Akwai kaddar tun Asali daga Ubangji

Idan Allah ya riga ya tsara komai to me Kake yiwa addu'a kenan? 
Kanason canja plan dinsa ne? 
Kai waye? 

Dole ne ka fahimci cewa kaddara ba wai wani dakin kurkuku ba ne wanda aka kulle ka a ciki aka jefar da mukullin ba, kaddara wani babban tsari ne na yiwuwar abubuwa (infinite possibilities) wanda ubangiji ya shimfida.

Addu'a ba kokari ba ne na canja shirin ubangiji, a'a, addu'a ita kanta tana daya daga cikin manyan makamashin da ke cikin shirin ubangiji tun farko.

Ka yi tunanin wannan: Allah ya riga ya kaddara cewa akwai wani alheri da yake jiran ka a wani mataki na rayuwarka, amma ya sanya "Addu'a" ta zama ita ce lambar sirri (code) da za ta bude wannan alherin.

Idan ba ka danna wannan lambar ba, alherin yana nan a ajiye, amma ba zai taba bayyana a gare ka ba. Don haka, addu'arka ba canja kaddara take yi ba; tana tabbatar da kaddarar da aka riga aka tsara maka ne ta hanyar dalili da sakamako.

A metaphysics, ana kallon ubangiji a matsayin wanda yake wajen lokaci. Ga Shi, babu "jiya" ko "gobe", komai yana faruwa ne a yanzu na Eternal Now.

Saboda haka, lokacin da kake addu'a a yau, Allah ya riga ya ji wannan addu'ar tun kafin halittar dukkan abubuwa, kuma ya riga ya saka amsar addu'ar taka a cikin tsarin rayuwarka.

Kuna gani? Ashe addu'a ba tawaye ba ne ga ikon Allah, ita ce kololuwar amincewa da ikon Sa da kuma shiga cikin babban shirin sa ta hanya mafi wayewa.

Makamashin da kake bayarwa yayin addu'a yana daidaita ruhinka da babban hasken kaddara. Duk lokacin da ka daga hannu, kana canja yanayin makamashin da ke kewaye da kai ne domin ya karbi abin da kake roko.

Rashin ilimi ne yake sa mutane su yi tunanin cewa tunda an rubuta komai to babu bukatar yin komai. Wannan shi ne babban kuskuren da yake tsare mutane a cikin duhun jahilci.

Shi kansa ilimi, makami ne. Kuma addu'a, ita ce ainihin amfani da wannan makamin na ilimi domin ka karkatar da kaddararka daga duhu zuwa haske, daga wahala zuwa nutsuwa.

A wannan shafin, za mu ci gaba da fasa kwan boyayyen ilimi.

Kada ka bari tsoro ko shakku su tsayar da kai. Addu'arka ita ce muryar ruhinka da ke magana da asalin inda ta fito, kuma wannan muryar tana da ikon girgiza dukkan kofofin da aka rufe maka.

Peace and Blessings.

Comments

Popular posts from this blog

duhu da haske

me yasa bazaka iya suffanta mutuwa ba bayan kamutu??

Gaskiyar Magana Akan pi network Dual 2 value