metaphysics
Me ya sa dole sai mun biya kafin mu kasance a raye?
A ilimin Metaphysics, an haife ka da yanci, amma duniya ta gina maka shamaki na makamashi wanda yake bukatar ka rika bayar da karfinka (energy) don kawai ka rayu.
An haife ka a duniyar da ba kai ka zaba ba, a tsarin da ba kai ka kera ba.
Wannan shi ne abin da muke kira The Matrix ko tsarin yaudara. An sa ka a cikin wani fili na wasa wanda ba kai ne ka tsara dokokin sa ba, don haka ruhinka yake jin ya takura tun daga ranar da aka haife ka.
Kana biyan kudin wurin kwana, ruwa, da abincin da kasar Allah take bayarwa kyauta.
Ruwan da kake biya, shi ne asalin rayuwarka. Lokacin da kake biyan kudi don abubuwan da dabi’a (nature) ta ba ka kyauta, kana mika ikon ruhinka ne ga masu iko da tsarin kudi.
Idan ba ka biya ba, tsarin zai nuna maka wanda ya mallake ka. Wannan shi ne tsoro (Fear vibration). Tsoro shi ne babban abin da yake toshe idon ruhin dan adam daga ganin gaskiya.
An ce maka haka abin yake: Yi aiki, ka samu kudi, ka biya kudin, kana ka sake maimaitawa.
Wannan shi ne zagayowar bauta (The cycle of samsara). Idan ba ka taba tambayar dalili ba, ruhinka zai kasance a kulle cikin wannan dabi’ar har abada.
Me ya sa rayuwarka take daure da bashi? Me ya sa 'yancinka yake da lissafin kudi duk wata?
Tambayi kanka Shin kana rayuwa ne don ka bauta wa bashi, ko kuwa an halicce ka ne don bautawa ikon ubangijinka?
Wannan ba tawaye ba ne, fadakarwa ce ta jiki.
Da zaran ka gano cewa kai ma kana da iko a akan kanka, za ka daina barin wannan tsarin ya rika juya makamashinka yadda yake so.
Za ka fara yin tambayoyi, za ka fara gina kariya, za ka fara tafiya da basira.
Anan ne ilimin Metaphysics yake fara aiki. Za ka fara amfani da tunaninka da kalaman bakinka don juya duniyar da take kewayen ka, maimakon ita ta rika juya ka.
Ba za ka iya canza dokokin duniya ba, amma za ka iya farkar da ruhinka daga barcin jahilci.
Duk wanda ya farka a ruhance, ko yana cikin wannan tsarin, shi 'yantacce ne.
Peace and blessings
Comments
Post a Comment